15 Yuli 2023 - 07:12
Ayatullah Afif Nabulsi, Aminin Imam Musa Sadr, Yayi Wafati

Ayatullah Afif Nabulsi shugaban kwamitin malaman Jabal Aamil na kasar Labanon ya rasu.



Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (A.S) ya nakalto daga Abna - Ayatullah "Afif Nabulsi", shugaban kwamitin malamai na Jabal Aamil Lebanon, Imam Juma'a na Saida, aminin Imam Musa Sadr kuma fitaccen dalibin Shahidi Muhammad Baqir Sadr a yau Juma’a 13 ga Yuli, 2023, bayan shafe tsawon shekaru ana fama rashin lafiya.

Wannan fitaccen malamin Shi'a na kasar Labanon ya kasance daya daga cikin fitattun masu kare gwagwarmaya kuma daya daga cikin abokan shahidai Sheikh Ragheb Harb da Sayyid Abbas Mousavi, wanda ya jagoranci kwamitin malamai na Jabal Aamil Lebanon har zuwa karshen rayuwarsa kuma ya ke jagorantar sallar Juma'a a birnin Saida dake kudancin kasar Lebanon

A yammacin yau Juma'a 13 ga watan Yuli 2023 ne za a gudanar da jana'izar Ayatullah Nabulsi a Majmau Zahra da ke birnin Saida a kudancin kasar Lebanon.

Za a gudanar da zaman makokin wannan fitaccen malamin ne a ranakun Asabar da Lahadi 14 da 55 ga Yuli, 2023, da karfe 10:00 na safe zuwa 12:00 na rana, da kuma karfe 16:00 na dare zuwa 19:30 na dare a cikin majma'a Zahra da ke garin Saida.

Yana da kyau a ambaci cewa Ayatullah Afif Al Nabulsi yana daya daga cikin manyan malaman kasar Labanon kuma mamba a majalisar koli ta shi'a ta wannan kasa. Ya kasance daya daga cikin wadanda suka kafa hukumar "Jabal Amel Scholars Board" tare da "Shahid Sheikh Ragheb Harb" wadanda suka ba da gagarumar gudunmawa wajen tallafawa gwagwarmayar Musulunci a kudancin Lebanon. Ana kuma dauki Al-Nabulsi a matsayin mamba a jagorancin kungiyar Hizbullah a lokacin babban sakataren kungiyar "Shaheed Sayyid Abbas Mousawi". Amma daga baya, ya fifita fannin koyarwa da ayyukan kimiyya da shiga harkokin siyasa kai tsaye.

......................